Ofishin jakadancin kasar Sin dake Madagascar ya fitar da wasu kan sarki masu dauke da hotunan wuraren ban sha'awa na kasar Madagascar da kuma na kasar Sin.
Jakadan jamhuriyar jama'ar kasar Sin, Yang Min, a yayin da yake jawabi a lokacin bukin gabatar da kan sarkin, ya ce, su kan sarkin wata sheda ce a zahiri, wacce ke nuni da abokantakar dake tsakanin kasar Sin da Madagascar.
Jakadan na kasar Sin ya yi fatan jama'a za su yi amfani da kan sarkin a kan ambulolin wasikun su, tare da kuma aje su a cikin kundin ajiyar su na jerin kan sarki.
Kamar dai yadda ministan Madagascar na sadarwar waya da wasiku da sabbin fasahohi, Andre Neypatraike ya bayyana, wadannan kawunan sarki wadanda ake saye a lika a kan ambulan domin aikewa da wasiku, masu fasahar kasar Sin ne da Madagascar suka zana tare da buga su. (Suwaiba)