in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin nune-nunen motoci na duniya na shekarar 2014a nan birnin Beijing
2014-04-21 16:25:18 cri

A ran 20 ga wata, an bude bikin nune-nunen motoci na duniya na shekarar ta 2014 a nan birnin Beijing, wanda za a shafe kwanaki 9 masu zuwa ana yinsa. Babban takensa shi ne, 'motoci su samar wa jama'a wata kyakkyawar makoma'. A matsayin bikin nune-nunen motocin mafi girma a kasar Sin da aka shirya bayan ko wadanne shekaru biyu, yawan fadin wurin nunin motocin, da kuma yawan sababbin motocin da aka nuna dukkansu ya kai wani sabon matsayi bisa tarihi.

A matsayin bikin baje fasahar kirar motoci mafi muhimmancin a duk duniya, wannan bikin ya jawo hankulan kamfanoni fiye da dubu 2 daga kasashe da yankuna 14 da suka halarci bikin, inda ake nune-nunen motoci da yawansu ya kai 1134.

Samfurar motoci kirar kasar Sin sun shiga cikin bikin nune-nunen motoci cikin yakini. Kamfanonin Sin ciki har da Kamfanin Dongfeng, da kamfanin motoci na farko wato Yiqi, da Chang'an, da BYD da dai sauran kamfanonin kasar Sin sun nuna sakamakon da suka samu na kirkire-kirkire.

A shekarar bara, yawan motocin da aka kere, da na sayar da su a kasar Sin, dukkansu sun wuce miliyan 21, sakamakon haka kasar Sin ta zama babbar kasuwa ta farko a duk duniya a cikin jeren shekaru 5 da suka gabata wajen sayar da yawan motoci. Hadaddiyar kungiyar motoci ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, karuwar yawan motocin da za a kere, da kuma sayar a shekarar 2014 a kasar Sin za ta kai kashi 8 zuwa 10 bisa dari. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China