A ranar 26 ga wata, aka kammala aikin kirkiro motocin bas masu aiki da lantarki a birnin Changchun da ke arewacin kasar Sin, wadanda kamfanin kirkiko na'urorin da ke tafiya kan hanyoyin kasa wato CNR ya dauki nauyin kirkiro su. Wadannan motoci na zamani sun zama karo na farko da kasar Sin ta fitar zuwa Afirka, kuma karo na farko da za a iya amfani da su a kan tudu mai tsayi na kasar Sin a fannonin motocin bas da ke aiki da lantarki na zamani da suke tafiya kan hanyoyin.
Za a yi amfani da wadannan motoci ne a kan hanyar farko a tsakanin biranen Habasha da sauran yankunan da ke kudu da hamadar Sahara.
Wani darektan kamfanin CNR Mista Liu Gang ya sanar da cewa, bisa yarjejeniyar da kasashen Sin da Habasha suka daddale, kamfanin CNR zai samar da irin wadannan motoci guda 41 ga kasar Habasha. (Danladi)