Mai yiwuwa ne tawagar tsaron kota-kwana, ta kasashen gabashin Afirka za ta soma aiki gadan-gadan, nan da watan Disambar karshen shekarar nan.
Tawagar ta EASF wadda ake fatan za ta kunshi sojoji da 'yan sanda da kuma wasu fararen hula, za ta tallafawa kasashen yankin ne, wajen magance kalubalen ayyukan ta'addanci.
An dai bayyana bukatar fara amfani da wannan tawaga ne, yayin taron yini uku da ministocin tsaro, da sauran wakilan kungiyar tsaron kasashen gabashin Afirka suka gudanar a ranar Laraba.
A jawabinsa ga mahalarta taron, ministan tsaron kasar Rwanda James Kabarebe, ya ce, akwai kyakkyawan tsari na musamman da aka tanada, domin tabbatar da nasarar aikin tawagar. Hakan a cewar sa zai tabbatar da nasarar burin da ake da shi, na dakile yaduwar manyan laifuka, ciki hadda fashin teku, da farautar namun dajin da dokokin kasashen suka haramta.
Bugu da kari tawagar za ta ba da gudummawa ta musamman wajen magance rikice-rikice, da wanzar da zaman lafiya.
Taron wanda aka gudanar a birinin Kigali ya samu halartar wakilai daga kasashen Rwanda, da Uganda, da Kenya, da Burundi, da Kamaru. Sauran sun hada da Jibouti, da Habasha, da Seychelles, da Somaliya da kuma Sudan. (Saminu)