Babban Sipeta 'yan sanda na kasar Kenya David Kimaiyo ya ce, shugabannin 'yan sanda na kasashen Afrika za su gana a birnin Mombasa, na kasar ta Kenya, daga ranar Litinin domin musayar ra'ayi a kan muhimman bayanai a kan 'yan ta'addanci da kuma masu aikata laifin, hada-hadar muggan kwayoyi, da kuma masu kashe namun daji.
Kimaiyo ya ce, taron na kwanaki biyar, ana sa rai zai tara shugabannin 'yan sanda da shugabannin bangaren binciken aikata laifuka na kasashen Afrika 17, domin tunkarar karuwar barazana ta tsaro a yankin.
Ya ci gaba da cewa, kwararru a kan harkokin tsaro daga kasashen Jamus da Turkiyya da Faransa da Aljeriya da Nigeria su ma za su halarci taron, domin samar da hanyoyin hadin kai na magance aikata manyan laifukka da ake hada kai a yi a kasashe dabam-dabam.
Ana sa rai taron zai samar da shawarwari mafi inganci da suka dace domin sa ido a kan al'amurran tsaro a yankin. (Suwaiba)