in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an sojin yammacin Afirka na taro kan tsaro
2014-09-11 10:57:07 cri

Kungiyar hadin kan yammacin Afirka ta ECOWAS ta kira wani taron manyan hafsoshin sojin yankin, domin tattauna muhimman batutuwan da suka jibanci tsaro.

Taron dai na yini uku wanda kuma shi ne karo na 34 da jami'an sojin yankin ke gudanarwa, na nazartar yanayin da ake ciki game da yaki da dakarun kungiyar nan ta Boko Haram a tarayyar Najeriya, da kuma yanayin siyasar kasahen Mali da Guinea Bissau.

Sauran batutuwan sun hada barazanar da mayakan kungiyoyi masu nasaba da Al-Qaida ke haifarwa yankin, da ta 'yan fashin teku, da ma batun tsaron tekun. Baya ga batun bullar cutar nan ta Ebola dake barazana ga rayukan dubban al'ummun yankin.

Cikin jawabinsa na bude taron, ministan tsaron kasar Ghana Benjamin Kunbuor, kira ya yi ga mahalarta taron da su zage damtse wajen ba da gudummawar dakile yaduwar cutar Ebola. Kunbuor ya ce, gwamnatin kasarsa na matukar lura da irin ci gaban da ake samu a wannan fanni, wanda hakan ne ma ya sanya Ghanan kasancewa cibiyar raba kayayyakin yaki da cutar.

A daya hannun kuma Mr. Kunbuor ya ce, kasar ta Ghana na sanya ido, tare da kula ga yanayin tsaro da ake ciki a arewa maso gabashin Najeriya, tare da nasarar shirin wanzar da zaman lafiya na ECOWAS a Guinea Bissau. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China