in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambiya ta rufe iyakokin kasarta bayan yunkurin juyin mulki
2014-12-31 12:00:10 cri

Kasar Gambiya ta rufe kan iyakokinta bayan wani yunkurin juyin mulki a cikin daren Litinin zuwa Talata.

Gambiya, karamar kasa ce dake yammacin nahiyar Afrika, da kasar Senegal ta kewaye, kuma suke raba iyaka bisa tsawon kilomita 740. Sojoji da 'yan sanda sun kafa tashoshin bincike a tsawon kan iyarkar, tare da hana duk motocin shiga cikin kasar.

Haka ne an rufe iyaka, za'a iyar sake bude iyakar nan da awa guda, in ji wasu majiyoyin tsaro. Rediyon kasa, Gambia Radio, da talabijin kasa sun dakatar da shirye shiryensu, sai kawai watsa kide kide. Manyan jami'an gwamnati, an ba su umurnin su tsaya gidajensu. Filin jirgen saman kasa da kasa dake birnin Banjul, guda tilo da kasar take da, shi ma an rufe, ko da yake ma'akatan filin jirgin saman sun ce, za'a iyar bude shi watakila nan da 'yan sa'o'i masu zuwa.

Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan fadar shugaban kasar da misalin karfe biyu zuwa uku na safe, bisa agogon wurin, an kashe biyar daga cikinsu, sannan wasu da dama suka ji rauni, haka kuma an cafke shida daga cikinsu.

Shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh na ziyarar aiki a yanzu haka a Dubai. Mista Jammeh ya hau karagar mulkin kasar tun a shekarar 1994, bayan wani juyin mulkin soja, Yahya Jammeh mai shekaru 49 da haifuwa, zai shiga takarar zaben shugaban kasa a wa'adi na biyar a shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China