A ranar Alhamis ne dai Gambiya ta sanar da cewa, ta yanke huldar diplomasiyya da yankin Taiwan bayan shekaru 18, kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya ce, ma'aikatar ta samu wannan labarin ne ta wasu kafofin yada labarai na kasashen waje domin Gambiya ba ta tuntubi kasar Sin ba game da hakan.
Mr. Hong ya ce, kasar Sin guda daya ce tak a duniya, amincewa da hakan da bin yadda yake abu ne da duk kasashen duniya suka sani, kuma ba da goyon baya ga kasar don ganin ta ci gaba da samun dawwamammen zaman lafiya da hadin kai, abu ne da ake bukata a ko da yaushe.(Fatimah)