in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta kashe miliyoyin dala domin murkushe matsalar yunwa a Gambiya
2014-03-11 11:59:41 cri

A halin da ake ciki dai, majalisar dinkin duniya ta shirya kashe miliyoyin dalolin Amurka domin bayar da agaji ga wadansu shirukka, wadanda za su murkushe matsalar yunwa dake addabar yara a kasar Gambiya.

An dai kaddamar da wadannan shirukka na dakile yunwa a Banjul, babban birnin kasar ta Gambiya, wace ke yammacin Afrika, inda kuma a kasar ne yara kasa da shekaru biyar ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, a daidai lokacin, da kasar ta Gambiya ke cikin wani hali na tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Ofishin majalisar dinkin duniya dake kasar ta Gambiya ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, suna muradin tabbatar da aiwatar da shirukkan, wadanda za su zama taimako ga gwamnatin Gambiya wajen kara kaimin kokarin da suke yi na yaki da matsalar yunwa dake addabar yara a kasar ta Gambiya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China