in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Gambiya ya ce, zai yiwa 'yan fursuna 19 ahuwa
2013-08-09 14:45:34 cri

Wata sanarwa da aka bayar ranar Alhamis na mai baiyana cewa, shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh zai yiwa 'yan fursuna 19 ahuwa.

Shugaban na Gambiya ya ba da wannan sanarwa ne a fadar shugaban kasa yayin da shugabannin addini suka kai masa ziyara a matsayin bukukuwan sallar Eid Ul Fitr.

Shugabannin addinin sun yi kira ga shugaban kasar da ya yi ahuwa ga wasu 'yan fursuna dake daure a gidan yarin Mile Two a kasar.

Daya daga cikin dattijan kasar Alieu Mboge ya ce, 'Muna kira gare ka ka yi ahuwa ga wasu 'yan fursuna dake daure a gidan yari saboda kai ne shugaba, don haka, muke rokonka kayi masu ahuwa.'

Ko da yake dai ba'a san ko su waye a kaiwa ahuwan ba, shugaban kasar ya kawar da dukkan wani tsammani na sakin tsohon ministan harkokin shugaban kasa Njogu Bah, tsohon ministan shari'a Lamin Jobarteh, da tsohon babban lauyan gwamnati Pa Harry Jammeh. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China