in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambia ba ta taba amfana daga shirin inganta cinikayya da Amurka ba
2014-12-30 10:15:58 cri

Gwamnatin kasar Gambia ta ce, ba ta taba amfana daga shirin bunkasa cinikayya tsakanin ta da kasar Amurka ba, don haka fidda kasar daga jerin kasashen da ka iya cin gajiyar manufar Amurkan ta AGOA, ba wani abun damuwa ba ne.

Wannan dai tsokaci na kunshe ne cikin wata sanarwa, da fadar gwamnatin kasar ta fitar, bayan da shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana fidda kasar daga tsarin na AGOA a ranar 23 ga watan nan.

A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2003 ne dai Amurka ta sanya Gambia cikin kasashen da ka iya cin gajiyar shirin cinikayya cikin 'yanci na AGOA, wanda ya tanaji baiwa kasashen yankin kudancin Saharar Afirka, damar shigar da hajojinsu Amurka ba tare da haraji ba. Kafin daga baya bayan nan a fidda Gambian, bisa zargin keta wasu hakkokin bil'adama.

Sai dai a hannu guda mahukuntan Gambian sun ce, Amurka ta kakabawa tsarin na AGOA wasu ka'idoji masu wuyar cikawa, ciki hadda alakanta cin gajiyar tsarin, da biyayya ga tsarin dimokaradiyya irin ta yammacin duniya, kana sai kayayyakin da suka dace da matsayin inganci na Amurka ne za a iya shigarwa cikin kasar, matakin da ya hana Zambiyan amfana daga waccan manufa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China