in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a kara yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar Ebola
2014-12-29 16:56:00 cri

A farkon shekarar 2014, babu wanda tsammanin cewa cutar Ebola da ta barke a karon farko a kasar Guinea za ta iyar yaduwa a sauran kasashen yammacin Afirka kamar Saliyo, da Liberia, har ma zuwa kasashen Amurka, Spaniya da sauran kasashen duniya. Me ya kawo dalilin yaduwar wannan cuta cikin sauri a duniya? Wane darasi ne dan adam ya rike, kuma wadannan irin fasahohi aka yi koyi da su wajen rigakafin wannan cuta da kuma hana sake abkuwar irin wannan bala'i?

Garmai Cyrus wata ma'aikaciyar jinya ce a wata cibiyar sa ido kan mutanen da suka kamu da cutar Ebola dake kasar Liberia. Tun daga aka fara samun cutar Ebola a kasarta, a kowace rana, ita da sauran abokan aikinta su kan zo ofis tare da rera waka da farko, sannan su fara aikinsu. Cyrus ta ce,"Lokacin da muke duba idanun wadanda suka kamu da cutar Ebola, ka ga jin tsoro a ciki kawai. Burina da aikina su ne baiwa wadannan mutane taimako da bayyana imani da kyakkyawan fata gare su, da kokarin ganin wannan cuta ta fita daga jikinsu da samun damar fita daga cibiyar."

A kofar cibiyar sa ido kan mutanen dake dauke da cutar Ebola dake gabashin kasar Saliyo, Erison Turay ya zo don ganin iyalansa dake wannan cibiyar masu fama da Ebola, ya ce,"Na ci sa'a, yanzu ina cikin koshin lafiya, amma 'yan uwana kusan 16 sun mutu a sakamakon cutar Ebola. A halin yanzu, ni da mamata da kanwata kawai muka rage cikin iyalin mu. Ina yin addu'a a kowace rana da fatan iyalaina su samu lafiya."

Erison yana da sa'a saboda cutar Ebola ba ta kashe shi ba. Amma mutane da dama ba su tsira ba daga hannun dodon cutar Ebola ba, suna kokari wajen yaki da cutar. Ya zuwa ranar 24 ga watan Disamba, an gano mutane kimanin dubu 20 da suka kamu da cutar Ebola a kasashe 8 wato Guinea, Liberia, Saliyo, Mali, Nijeriya, Senegal, Amurka da kuma Spaniya, yayin da kuma mutane 7588 a cikinsu suka mutu sakamakon cutar. A hakika dai, bisa yanayi mai tsanani da ake ciki na fama da cutar Ebola, a ranar 8 ga watan Agusta, babbar direktar hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Margaret Chan ta sanar da cewa, cutar Ebola ta kasance a matsayin batun kiwon lafiya a duniya da ya faru ba zato ba tsammani tare da jawo hankalin kasa da kasa sosai. Margaret Chan ta bayyana cewa,"Cutar Ebola ta fi kawo tasiri da yin tsanani a shekaru kimanin 40 da suka gabata a duniya. Na amince da shawarar da kwamitin hukumar WHO mai kula da harkokin gaggawa ya bayar, wato ba da sanarwar mai da cutar Ebola a matsayin batun kiwon lafiya na duniya da ya faru ba zato ba tsammani dake jawo hankalin kasa da kasa sosai."

Ba cutar Ebola ta kashe mutane da dama kawai ba, hatta ma ta kawo babbar illa ga tattalin arziki a kasashe masu fama da ita. Bisa rahoton da bankin duniya ya gabatar a ranar 2 ga watan Disamba, ana sa ran cewa, tattalin arzikin kasashen Liberia, Saliyo da Guinea a shekarar 2015 zai ragu, watakila wadannan kasashen uku za su sake bukatar taimako da basussuka daga kasashen waje wanda a baya ba su bukatar hakan.

Tun barkewar cutar Ebola, kasa da kasa sun kiyaye bada gudummawa ga yankin kasashen yammacin Afirka mai fama da cutar Ebola da yin nazari kan allurar rigakafin cutar. Kasar Sin ta bada tallafin kudi da kayayyaki ga kasashen yammacin Afirka, tare da tura tawagogin likitoci zuwa wannan yankin. A ranar 15 ga watan Nuwanba, tawagar likitoci ta sojojin kasar Sin ta isa Monrovia, babban birnin kasar Liberia. Ministan harkokin wajen kasar Liberia Augustine Kpehe Ngafuan ya yi maraba da zuwan tawagar da cewa,"Kafin cutar Ebola ta bullo, tun fil azal gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun kasance abokai ne na jama'ar Liberiya, kana a yayin da cutar ta fara yaduwa a kasarmu, kuma jama'ar kasar Sin da gwamnatinta sun cigaba kasancewa abokan mu. Kana sun yi alkawari cewa, za su ci gaba da zama abokan mu har sai an kawar da cutar daga kasarmu, wannan ne hakikanin zumunta a tsakaninmu."

A karkashin kokarin da dukkan duniya ta yi, an rage saurin yaduwar cutar Ebola a kimanin shekara daya bayan barkewar wannan cuta, kasashen Nijeriya, Senegal bi da bi ne suka fita daga cikin kasashe masu fama da cutar Ebola. John Jameson, wani mai binne gawawwakin mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola a birnin Monrovia dake kasar Liberia, ko da yake yana cin karo da gawawwaki a kowace rana, amma a idonsa, dan Adam zai cimma nasarar yaki da cutar a karshe, kuma sai dai dan Adam ne kawai zai iyar warware matsalolin duniya da kansa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China