141203-Sin-ta-mikawa-MDD-Dala-miliyan-6-domin-yaki-da-cutar-Ebola-Kande.m4a
|
A jiya Talata 2 ga watan nan na Disamba ne gwamnatin kasar Sin ta daddale wata yarjejeniya da hukuma mai kula da ayyukan ci gaba ta MDD wato UNDP, yarjejeniyar da ta kunshi baiwa Asusun amintattu na yaki da cutar Ebola dake samun taimakon sassa da dama, tallafin kudi har dala miliyan 6.
A wannan rana ta Talata ne dai ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ta wakilci gwamantin kasar wajen daddale wannan yarjejeniya da ofishin MDDr.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kudi dala miliyan shida, suna cikin matakan taimako karo na hudu, da gwamnatin kasar Sin ta samar domin yaki da cutar Ebola, wanda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya alkawarta bayarwa a 'yan kwanaki baya.
Ana kuma sa ran amfani da kudaden ne wajen taimakawa tawagar musamman ta MDD wajen ci gaba da yaki da cutar ta Ebola. Bayan kammala rattaba hannu kan yarjejeniyar, babban wakilin hukumar kula da ayyukan ci gaba ta UNDP da ke kasar Sin Alain Noudehou, ya zanta da 'yan jarida inda ya ce,
"Tawagar musamman ta MDD za ta yi amfani da wannan kudin tallafi dala miliyan 6 da kasar Sin ta samar cikin ayyukanta biyu. Daya aikin shi ne inganta manufofin shawo kan cutar Ebola a kasashen da ke yammacin Afirka. Wato na taimaka wa wadannan kasashe wajen sayen wasu na'urorin sanya ido kan cutar, da kuma baiwa masu dauke da cutar tufafin kariya. Da kuma taimakawa unguwannin da ke wadannan wuraren samun damar farfadowa bayan kawo karshen cutar, da kuma kyautata karfinsu na yaki da cuttuttuka."
Tun bayan barkewar cutar Ebola, kasar Sin ta taimakawa ayyukan jin kai ga kasashe masu fama da cutar a watan Afrilu, da na Agusta, da na Satumba, da kuma na Oktobar bana, tallafin da bisa jimilla darajarsu ta kai Yuan miliyan 7500, baya ga tura kwararru da masu jinya 700 zuwa kasashen. Aikin da kasashen Afirka 13, da MDD, da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, da kuma kungiyar tarayyar Afirka ta AU suka hada gwiwar aiwatarwa.
Wannan sabuwar yarjejeniya, ta nuna aniyar kasar Sin wajen kara himma da kwazo, a fagen tinkarar kalubalen kiwon lafiya da ke gaban duniya.
A cewar Mr. Noudehou kasar Sin ta cancanci yabo bisa irin taimakon da take baiwa kasashen da ke yammacin Afirka, a yakin da suke yi da cutar Ebola. Ya ce
"Muna farin cikin ganin yadda kasar Sin ta shige gaba, a aikin da ake yi na yaki da cutar Ebola, inda ta samar da dimbin kayayyaki, da kudade na shawo kan yaduwar cutar. Kawo yanzu kasar Sin ta riga ta samar da Yuan miliyan 7500 domin aikin. Bisa yarjejeniyar ba da tallafin kudi da muka daddale yau, da dala miliyan biyu da kasar Sin ta bai wa WHO, da kuma dala miliyan 6 da Sin ta bai wa hukumar kula da hatsi ta MDD, tabbas za a kara azama sosai ga kasashen da ke yammacin Afirka, wajen yaki da cutar Ebola."
A nasa bangare kuma mai ba da taimako ga ministan kasuwancin kasar Sin , Zhang Xiangchen, ya gabatar da shirin taimako da kasar Sin ta tanadarwa kasashe masu fama da cutar a nan gaba, inda ya ce,
"Game da shirinmu a nan gaba, idan har ba a kai ga kawar da cutar Ebola ba, to kasar Sin ba za ta dakatar da bada taimako ba. za mu dora muhimmanci kan inganta hadin gwiwarmu da Afirka ta fuskar kiwon lafiya daga dukkan fannoni a cikin tsahon lokaci. Za mu taimakawa kasashen Afirka, wajen kyautata kwarewarsu ta kandagarki, da dakile cututtuka masu yaduwa da su kan barka ba zato ba tsammani, gami da kyautata tsarinsu na kiwon lafiyar jama'a. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin za ta mai da hankali kan aikin farfadowar kasashen bayan cutar, inda za ta ba da tallafi ga kasashen Afirka gwargwadon karfinta a fannonin kafa tsarin kiwon lafiyar jama'a, da raya muhimman ayyukan more rayuwa, gami da taimakawa kasashe masu samun tallafi wajen farfado da tattalin arzikinsu."(Kande Gao)