in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin Najeriya
2014-12-25 16:40:39 cri

Asusun ba da lamuni na IMF ya fidda wani rahoto a kwanakin baya, inda ya yi hasashen cewa, yawan karuwar tattalin arzikin tarayyar Najeriya a shekarar 2015 zai yi kasa zuwa kashi 5%.

Asusun ba da lamuni na IMF ya ce a badi, mai yiwuwa ne yawan karuwar tattalin arzikin Najeriya zai ragu zuwa kashi 5%, sabanin karuwar da ya samu zuwa kashi 6.1% daga watan Yuli zuwa na Satumbar bana.

Kamar yadda aka bayyana a cikin wannan rahoto, dalilin da ya sa asusun na IMF ya yi wannan hasashe shi ne, yiwuwar faduwar farashin danyen mai a kasuwannin kasa da kasa wanda ka iya kaiwa kashi 25% a shekarar mai zuwa, matakin da zai rage yawan kudaden shigar da Najeriya ke samu, kasancewar tattalin arzikin kasar na dogaro ne kan harkar hakar man fetur, kana hakan zai tilasawa gwamnatin kasar daukar matakan tsimin kudi, yayin da take aiwatar da kasafin kudinta.

Har wa yau kuma, wata matsalar da asusun IMF ya ambata cikin rahotonsa ita ce, Najeriya za ta iya fuskantar matsalar ficewar masu zuba jari daga kasar, sakamakon rashin cikakkiyar masaniya ga masu zuba jarin, dangane da yanayin da farashin man fetur, da tattalin arzikin kasar zai kasance ciki a nan gaba, saboda haka ake hasashen za su iya kauracewa kasuwannin kasar, domin kaucewa wasu hadurra da za su iya fuskanta.

Sai dai a cikin rahotonsa, asusun na IMF ya ce gwamnatin Najeriyar ta riga ta dauki wasu matakai a fannonin harkar kudade, da na kasafin kudin ta, domin kaucewa matsalar da raguwar kudin shigar da take samu a fannin man fetur ka iya haddasawa, da matsin lambar da kudin kasar Naira yake fuskanta, matakin da ke tilasawa Nairar raguwar daraja, da kiyaye kudaden kasashen waje da Najeriya ta ajiye, ta yadda za a samu damar tabbatar da ingancin yanayin tattalin arzikin kasar.

Kamar yadda asusun IMF ya fada, wadannan matakan da mahukuntan Najeriyar ke dauka sun hada da daidaita darajar musayar kudi, inda kafin daukar wannan mataki, da dalar Amurka daya ana iya samun Naira 155, amma a yanzu dala daya ta koma Naira 168. Sauran matakan da aka dauka sun kunshi kara gibin da darajar kudin za ta iya samu, da kara yawan kudin ruwan da za a iya samu bisa ajiyar kudi da kashi 1%.

Haka kuma an bukaci kamfanoni masu zaman kansu da su kara ajiye tsabar kudi, ta yadda yawan tsabar kudin ajiyar su zai karu zuwa kashi 20% daga kashi 15%. Bisa wadannan matakai da aka dauka IMF din ya nuna amincewa da kwazon mahukuntan kasar.

Ban da haka kuma, cikin wannan rahoto, asusun na IMF ya tunatar da gwamnatin Najeriyar bukatar kara mai da hankali kan wasu sassan da za su iya haddasa raunanar tattalin arzikin kasar, bisa la'akari da yanayin da kasar take ciki na rashin isasshen karfi, na tinkarar tangal-tangal da yanayin farashin man fetur ke fuskanta, gami da sauyin yanayi na sha'anin hada-hadar kudade ta kasa da kasa.

Don gane da hakan ne asusun IMF ya yi kira ga gwamnatin Najeriyar da ta lura da duk wani canji a yanayin tattalin arzikin duniya, don magance wasu hadurra da za su iya bullowa ba zato ba tsammani, wadanda kuma za su iya gurgunta tattalin arzikin kasar. Game da kasuwannin cikin gidan kasar kuwa, asusun na IMF ya bukaci hukumomin kasar, da su lura da jarin dake kokarin barin kasar, da batun raguwar kudin shiga a bangaren harkar man fetur, wadanda ke dada matsawa tattalin arzikin kasar da tsarin kudadenta lamba.

Haka zalika, asusun na IMF ya bayyana cewa kudaden ajiyar rarar danyan mai da Najeriyar ke tarawa, wato "Excess Crude Account" a Turance, ya taba kaiwa dalar Amurka biliyan 21, yayin da kasar ke tinkarar babbar matsalar hada-hadar kudi ta shekarar 2008. Sai dai a wannan lokaci kudin da ke cikin wannan asusun ajiya ya ragu zuwa dala biliyan 3 kacal. Bisa hakan ne kuma asusun na IMF ya shawarci gwamnatin kasar da ta kara kudin ajiyar na ta a wannan asusu, ta yadda za ta samu isasshen kudin da za ta iya amfani da shi a nan gaba, lokacin da take tinkarar wata matsalar ta ba-zata.

Ban da haka, asusun na IMF ya tunatar da mahukuntan Najeriyar, game da bukatar shawo kan hare-haren ta'addanci dake addabar wasu sassa na kasar, da batun daukar matakan magance abkuwar duk wani tashin hankali, yayin babban zaben kasar dake tafe a farkon shekarar 2015 mai zuwa.

A karshen rahoton na sa, asusun na IMF ya jaddada cewa, cikin tsahon lokaci a nan gaba, batun ko tattalin arzikin Najeriyar zai samu ci gaba ko akasin haka, ya dogaro ne kacokan, ga ko kasar za ta iya rage dogaron tattalin arzikin ta kan harkar cinikayyar danyen man ko a'a. Da kuma kwarewarta ta kara janyo hankulan masu zuba jari, zuwa sauran bangarori da ba na man fetur ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China