in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi murnar bikin Tsakiyar Yanayin Kaka a Najeriya
2014-09-09 16:26:17 cri


Ranar 8 ga watan Satumbar bana, rana ce ta bikin Tsakiyar Yanayin Kaka ta al'ummar Sinawa, wato mid-autumn festival a turance. A cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, an shirya wani gagarumin biki don murnar zagayowar wannan rana, tare da ilmantar da al'ummar Najeriya game da al'adun bikin Tsakiyar Yanayin Kaka. Wannan biki na murnar zagayowar ranar Tsakiyar Yanayin Kaka ya samu halartar dubban jama'a, ciki har da 'yan Najeriya masu sha'awar koyon harshen Sinanci, da jami'ai daga ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da kuma wakilai daga wasu kamfanonin kasar Sin dake Abuja.

A wajen bikin, an nuna hoton bidiyo game da al'adun bikin Tsakiyar Yanayin Kaka na kasar Sin, inda aka bayyana wasu al'adun gargajiya masu alaka da wannan biki, kamar su haduwa da iyali, cin wani nau'in abinci mai suna Yuebing; wato wainar wata a hausance da makamanta.

Akwai kuma wasu 'yan Najeriya guda uku wadanda suka taba yin karatu a kasar Sin, wadanda suka bayyana abubuwan da suka ji suka gani, game da yadda al'ummar Sinawa ke gudanar da wannan biki na Tsakiyar Yanayin Kaka. Wata 'yar Najeriya mai suna Obiageri Henshaw data taba yin karatun harshen Sinanci na tsawon shekaru 8 a kasar Sin, ta ce koda yake ta riga ta koma Najeriya, amma ba za ta manta da yaren Sin, da wainar wata na bikin Tsakiyar Yanayin Kaka ba.

Shi ma wani dalibi mai koyon harshen Sinanci a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja mai suna Eze Peter, ya karanta wata rubutacciyar wakar da ta shafi bikin Tsakiyar Yanayin Kaka cikin Sinanci, inda ya bayyana dalilin da ya jawo sha'awarsa ga koyon Sinanci.

A nasa bangaren, wani jami'in hukumar kula da harkokin ilimin sakandare a babban birnin tarayyar Najeriyar Abuja malam Yakubu ya bayyana cewa, koda yake ya sha zuwa kasar Sin amma bai taba samu damar halartar bikin Tsakiyar Yanayin Kaka na al'ummar Sinawa ba. Amma a wannan karo ya ji dadin riskar wannan biki a gida.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China