in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Najeriya na fuskantar kalubale sakamakon faduwar farashin man fetur
2014-10-31 16:32:46 cri

Sakamakon sauyin da aka samu a bukatun kasuwanni, wannan ya sa farashin man fetur ya fadi a kasuwannin duniya a karshen rabin shekarar da muke ciki, inda farashin ya fadi daga dalar Amurka 114 a watan Yuni zuwa dala 85 a yanzu, hakan ya sanya kasar Najeriya, wadda ta ke kan gaba wajen fitar da man fetur a yammacin Afrika, kuma tattalin arzikinta ke dogaro sosai kan fitar da man fetur take fuskantar babban kalubale.

Bisa kididdigar da wani jami'in majalisar kungiyoyin 'yan kasuwa da masana'antu reshen jihar Lagos ICCI ya bayar an ce, kashi 95 cikin 100 na kudin musanya, da kashi 85 cikin 100 na kudin shiga da kasar ke samu na dogaro ne kan fitar da man fetur. Saboda haka, faduwar farashin man fetur da aka fuskanta a wannan karo ta shafi bangaren tattara kudin musanyan kasar kai tsaye da kuma kudin shigar da ta ke samu. Bayan haka kuma, ta tilastawa gwamnatin kasar Najeriya ta saka kudin musanya da ta tanada, domin cika gibin kudin da ta samu, da kuma fuskantar faduwar darajar kudin kasar wato Naira sakamakon faduwar farashin man fetur, lamarin da ya jawo raguwar kudin musanya da kasar ta tanada. Babban bankin kasar Najeriya ya bayar da kididdigar cewa, yawan kudin musanya da kasar ta tanada a karshen watan Satumba ya kai dalar Amurka biliyan 39 da miliyan 604, amma ya zuwa karshen watan Oktoba, ya ragu zuwa dala biliyan 39 da miliyan 3, wato ya ragu da dala miliyan 601 a cikin wata guda.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Najeriya suka bayar, an ce, ko da yake farashin man fetur a kasuwanin duniya ya fadi zuwa matsayin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru kusan hudu da suka gabata, amma duk da haka wasu kwararru suna ganin cewa, farashin zai ci gaba da faduwa, inda ake ganin zai fadi zuwa dalar Amurka kimanin 70 kan kowace ganga a farkon shekarar 2015. Saboda haka, kwararrun sun yi hasashen cewa, hakan zai tilastawa babban bankin kasar daukar matakai, ciki har da kara yawan adadin kudin ruwa, da ci gaba da amfani da kudin musanya, da kuma amincewa da faduwar darajar kudin kasar wato Naira, da dai sauransu. Game da hakan, gwamnan babban bankin kasar Najeriya Godwin Emefiele ya bayyana cewa, hukumomin kudi na kasar na shirin daukar matakan da suka dace, da nufin ba da tabbaci ga daidaituwar farashin kayayyakin cinikayya, da kokarin rage tasirin da faduwar farashin man fetur ke haifarwa tattalin arzikin kasar. A waje guda, ministar kudin kasar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa, idan farashin man fetur ya ci gaba da faduwa, to gwamnatin kasar za ta rage kudaden da ta ke kashewa

Wannan yanayin da kasar ta Najeriya ke ciki ya sanya wasu mutanen da batun ya shafa kara fahimtar tsanantar matsalar da kasarsu ke fuskanta, wato yadda faduwar farashin man fetur ya yi tasiri ga tattalin arzikin kasar, sun kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da manufofin yin kwaskwarima kan tattalin arziki, don rage dogaro kan fitar da man fetur.

'Dan majalisar dattawa a kasar Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya yi kira ga gwamnatin da ta mai da hankali kan wannan batu, ya kuma baiwa gwamnatin shawarar da ta waiwayi tarihi domin ta koyi darasi, da kuma daukar matakan da suka dace, domin warware matsalolin da suka dade suna kawo barazana ga tattalin arzikin kasar, ciki har da rashin ingantaccen tsarin tattalin arziki, da dai sauransu. Babban jami'in zartaswa na kamfanin da ba shawarwari na kasar Najeriya na BIC Dr. Boniface Chizea ya nuna cewa, wasu dalilai kamar aikin hako iskar gas daga dutsen shale da kasar Amurka ke yi, da dai sauransu dukkansu na iya zama dalilan da suka haddasa faduwar farashin man fetur a duniya, ko da yake suna iya haddasa tabarbarewar tattalin arzikin kasar Najeriya, amma mai yiwuwa ne za su sanya kasar ta dauki matakan bunkasa tattalin arzikinta ta hanyoyi daban daban, hakan ba za ta ci gaba da dogaro kan masana'antun man fetur ba.

Game da batun sana'ar man fetur, inganta masana'antun tace danyen man kasar, shi ma na da amfani wajen warware matsalar. Shugaban kungiyar dillalan mai masu zaman kansu a Najeriya Chinedu Okorokwo ya bayyana a kwanan baya cewa, ana iya rage tasirin da faduwar farashin man fetur ke haifarwa tattalin arzikin kasar Najeriya ta hanyar kafa kamfanonin tace man fetur a kasar. Ya gabatar da cewa, yanzu ana shirin kafa irin wadannan kamfanoni a jihohin Kogi, da Bayelsa na kasar. Bayan da suka soma aiki, za su iya taimakawa kasar wajen rage kudin da take kashewa wajen shigo da man fetur din da aka tace, a sa'i daya kuma za a iya kara samar da guraban aikin yi, har ma da farfado da tattalin arzikin kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China