in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta amince da bukatar samun 'yancin kan Palasdinawa, in ji Abbas
2014-12-24 14:22:50 cri

Shugaban hukumar mulkin Palasdinawa Mahmoud Abbas wanda ya kai ziyara Algeri jiya Talata, ya kara jaddada cewar, za su yi kokarin ganin cewar, bukatar Palasdinawa ta kafa kasar kansu ta samu nasarar amincewar MDD.

A yayin da yake jawabi a wani taro da aka yi a hedkwatar ma'aikatar harkokin waje ta Algeriya, Abbas ya ce, bukatar da za su gabatar a gaban MDD na da niyyar kwato 'yancinsu a bisa yarjejeniyar kan iyaka ta shekarar 1967 da Isra'ila.

Jawabin na shugaban Palasdinawan ya kawo karshen ziyarar da ya kai Algeria ta kwanaki 3, wacce aka sadaukar wajen gabatar da nasarorin da aka samu na baya-bayan nan a game da fafutukar Palasdinawa.

Taron ya samu halarcin manyan jami'ai daga kasashen biyu. Abbas ya bayyana cewar, Isra'ila na ci gaba da kaucewa kaddamar da yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu a can baya, kuma hakan na ci gaba da dakile kokarin da ake yi na girka zaman lafiya.

Shugaban Paladinawan ya ce, kara gina zirin Gaza wanda Isra'ila ta wargaza a cikin hare-haren da ta kai na kwanaki 50 shi ne abu mafi mahimmanci a halin da ake ciki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China