in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Abbas ya bukaci MDD ta baiwa Falasdinawa kariya
2014-07-14 10:00:13 cri

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya bukaci MDD, da ta dauki matakan baiwa Falasdinawa kariya, sakamakon ci gaba da luguden wuta da Isra'ila ke yi kan yankunan Falasdinawa fafaren hula.

Shugaba Abbas ya mika wannan bukata ne dai ta cikin wata takarda da ya damkawa wakilin babban magatakardar MDD a Gabas ta Tsakiya Robert Serry, yayin wata ganawa da suka yi a jiya Lahadi.

Har wa yau jim kadan da kammala ganawar tasu, Abbas ya shaidawa manema labarai cewa, har ya zuwa yanzu, Isra'ilan na kaddamar da sabbin hare-hare, lamarin da ke kara yawan asarar rayuka da jikkatar mutane, baya ga barnata dukiyoyi da hakan ke haifarwa.

Rahotannin baya bayan nan daga zirin Gaza na cewa, wasu hare-hare uku da Isra'ila ta kaddamar a daren jiya Lahadi, sun hallaka mutane 4, ciki hadda wani mutum da dansa a kudancin yankin.

Yanzu haka dai adadin mutanen da hare-haren Isra'ilan suka hallaka ya kai mutane 170. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China