in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Falasdinu ya kara ja da baya
2014-09-04 14:40:36 cri

A cikin wani rahoto kan ba da tallafi ga al'ummar Falasdinu da aka fitar a ranar Laraba, taron MDD kan kasuwanci da cigaba (CNUCED) ya yi la'akarin cewa, tattalin arzikin Falasdinu da ke cikin mawuyacin hali, ya kara ja da baya a shekarar 2013 da ta 2014, musammun ma dalilin cigaba da gina matsugunnan Yahudawa da Isra'ila take yi. Tabarbarewar tattalin arzikin Falasdinu din na bayyana ja da bayan bunkasuwa, karancin kudi, tilastawa a fannin dogaro da tattalin arzikin Isra'ila, matsalar rashin aikin yi, karancin abinci da talauci.

Adadin bunkasa na shekara ta fuskar GDP na Falasdinu ya fadi, daga kashi 11 cikin 100 a shekarar 2010 da 2011, zuwa kashi 1,5 cikin 100 a shekarar 2013. Adadin da ya yi kasa sosai da na karuwar al'ummar Falasdinu, lamarin dake kara janyo raguwar kudin shiga ga ko wane mazauni.

Haka kuma, adadin rashin aikin yi ya karu sosai da kashi 36 cikin 100 a yankin Gaza, kana da kashi 22 cikin 100 a yammacin gabar kogin Jordan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China