in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abbas ya yi kira da a gudanar da taron gaggawa game da hare-haren Isra'ila a Gaza
2014-07-21 10:02:49 cri

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya yi kira ga kwamitin tsaron MDD, da ya kira taron gaggawa domin kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kaddamarwa a zirin Gaza.

Shugaba Abbas, wanda ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, ya ce, Falasdinawa na cikin wani irin matsanancin hali, da ya wajaba dukkanin kasashen duniya su ba da tallafin kawo karshensa.

Shugaban na Falasdinu ya kuma ce, akwai bukatar dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, su kauracewa sanya siyasar shiyya ko ta kasa da kasa, cikin wannan rikici dake salwantar da rayukan fararen hula.

A daya bangaren kuwa, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, cewa ya yi, bangaren kasarsa na tuntubar dukkanin wadanda wannan batu ya shafa, a kokarin da suke yi na dakatar da hare-hare a Gaza. Netanyahu ya ce, suna daukar dukkanin matakai na diplomasiyya da na soji, a lokaci guda kuma shugaban Falasdinawa na iya shiga shirinsu na lalubo hanyar tsagaita wuta, muddin ya fahinci cewa, Hamas ba ta da niyar cimma kudurin wanzar da zaman lafiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China