in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta nuna takaici kan rikicin da ke ci gaba a Sudan ta Kudu
2014-12-16 10:49:18 cri

Kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD ta bayyana bakin cikinta a game da rikicin da ake ci gaba da fafatawa a Sudan ta Kudu, wanda a yanzu haka an yi shekara guda cif, ana gwabza shi a jaririyar kasar ta Sudan ta Kudu.

Kungiyar IGAD ta zamanto mai shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu tun bayan da rikicin ya balle shekara guda da ta wuce.

Babban mai shiga tsakani na kungiyar Mr. Seyoum Mesfin, a yayin da yake jawabi ga 'yan jarida a Addis Ababa na Habasha ya ce, yankin na gabashin Afrika ya yi shekara guda yana fama da wannan matsala ta yaki a Sudan ta Kudu, to amma kuma ya yi kira ga daukacin 'yan kasar Sudan ta Kudu kada su lamunta da kara mai da su cikin hali na yaki da ramuwar gayya da hallaka jama'a da dukiyoyinsu.

Mr. Mesfin ya kuma bukaci 'yan kasar ta Sudan ta Kudu da su kaucewa sauraren jita-jita da kiyayya, wacce ka iya jefa kasar cikin mawuyacin hali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China