Shugaban manzonnin musamman na kungiyar IGAD game da wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu yanzu haka yana birnin Juba, tare da wata tawaga domin gudanar da shawarwari da gwamnatin Sudan ta Kudu da kuma sauran bangarori masu ruwa da tsaki kan manufar sake maido da shirin zaman lafiya a birnin Addis Abeba na Habasha a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
Cibiyar manzonnin musamman ta kungiyar IGAD game da kasar Sudan ta Kudu ta bayyana a ranar Lahadi da yamma a cikin wata sanarwa cewa, tana allawadai da harin gungun adawa na APLS/MPLS da ya kai kan wasu sansanonin sojojin gwamnati a yankin Nasir a ranar 20 ga watan Juli. (Maman Ada)