in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta sanar da fara tattaunawa tsakanin sassan da ke fada da juna a Sudan ta Kudu
2014-01-06 10:35:18 cri

Kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka (IGAD) ta sanar da dewa, an fara tattaunawar wanzar da lafiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, tsakanin sassan da ke gwabza fada da juna a Sudan ta Kudu.

Wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ta IGAD jakada Mahboub M. Maalim ya bayar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, ya ce, bayan kwanaki biyu da aka shafe ana tattaunawar, an kai ga gano muhimman batutuwa tare da cimma wasu yarjejeniyoyi.

Ya ce, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan wasu batutuwa guda biyu, na farko dakatar da fada, sai kuma batun wadanda ake tsare da su.

Kungiyar ta bayyana tabbacin cewa, tattaunawar za ta haifar da mai ido, ta yadda za a hanzarta mai ido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sudan ta Kudu.

Alkaluma na nuna cewa, kimanin mutane 1,000 ne suka halaka, kana wasu 200,000 suka rasa gidajensu tun lokacin da aka fara fadan tsakanin sassan biyu a Juba, babban birnin kasar, kana daga bisani ya bazu zuwa wasu sassan kasar.

Fadan dai ya barke ne, lokacin da shugaba Salva Kiir ya yi zargin cewa, sojojin da ke biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Machar da ya kora a watan Yulin shekarar da ta gabata, sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsa.

Shi dai Kiir, 'dan kabilar Dinka ne, yayin da Machar ya fito daga kabilar Lou Nuer, kuma rahotanni na cewa, yanzu fadan ya rikide zuwa fadan kabilanci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China