in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta gudanar da taro kan Sudan ta Kudu
2014-03-14 09:45:50 cri

Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya ce, kungiyar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afirka ta IGAD, na daukar karin matakan warware rikicin kasar Sudan ta Kudu.

Hailemariam wanda ya bayyana hakan yayin taron mambobin kungiyar karo na 25, da ya gabata a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, ya ce, IGAD ta yi matukar damu da halin kunci da fararen hula ke ciki a kasar.

Ya ce, duk da rattaba hannu da aka yi kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin kasar biyu makwanni 6 da suka gabata, kawo yanzu akwai sauran rina a kaba.

Har ila yau gabanin rufe wannan taro, an tattauna kan rahoton da jagoran masu shiga tsakanin na kungiyar Ambasada Seyoum Mesfin ya gabatar, kan batun kasar ta Sudan ta Kudu. Inda cikin jabawinsa, Mesfin, ya sake jaddada kiran kungiyar ta IGAD don gane da bukatar tsagin gwamnati da na 'yan tawayen kasar, kan batun martaba waccan yarjejeniya yadda ya kamata.

Taron na wannan karo, wanda firaministan kasar Habasha Hailemariam ya jagoranta, ya samu halartar shuwagabannin kasashen Uganda, da Kenya, da Sudan, da Sudan ta Kudu, da Djibouti da kuma firaministan Somaliya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China