in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta tsayar da wanda zai mata takarar shugaban kasa
2014-12-12 09:18:38 cri

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya (APC) ta tsayar da tsohon shugaban mulkin sojin kasar Janar Muhammadu Buhari mai ritaya a matsayin wanda zai mata takarar shugabancin kasar da zai fafata da shugaban Goodluck Jonathan da ke neman wa'adi na biyu a zaben da za a yi a kasar a shekara mai zuwa.

Sama da wakilan jam'iyyar 7,000 ne suka hallara a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin kasar don zabar mutumin da zai kalubanci shugaba mai ci.

Bayanai na nuna cewa, Buhari ya samu cancantar tsayawa ne bayan da ya samu kuri'u 5,000, abin da ya ba shi damar da doke tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da takwaransa na jihar Imo Rochas Okorocha da kuma mawallafin jaridar nan ta Leadership a Najeriya Sam Nda-Isaiah.

A ranar Labara ne yayin babban taron da ta gudanar a Abuja, jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta tsayar da shugaba Jonathan ba tare da hamayya ba a matsayin wanda zai mata takara a zaben da zai fafata da janar Buhari a shekara mai zuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China