in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya na shirin sake tsayawa takara
2014-10-30 10:51:04 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya ya fara shirye-shiryen neman sake tsayawa takarar jagorancin kasar, yayin babban zaben kasar dake tafe a farkon shekarar mai zuwa.

Wasu kafofi daga kasar sun bayyana cewa, ana sa ran shugaban kasar zai yanki katin neman yiwa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar takara ne da yammacin ranar Laraba.

Har wa yau wata majiya daga fadar gwamnatin kasar na cewa, tuni shugaban kasar ya bayyana wa jagororin jam'iyyar ta PDP aniyarsa, ta sake neman tsayawa takarar kujerar jagorancin kasar.

Hakan kuma na zuwa ne bayan da hukumar gudanar da zaben kasar mai zaman kanta INEC, ta tsaida ranar 30 ga watan nan na Oktoba a matsayin ranar karshe ta yankar katin neman tsayawa takarar jagoracin kasar.

Dama dai an yi hasashen takarar shugaba Jonathan, tun bayan da kusoshin jam'iyyarsa ta PDP suka bayyana goyon bayansu gare shi, na ya sake yiwa jam'iyyar takara.

Tuni dai hukumar zaben kasar ta sanya ranar 14 ga watan Fabarairun shekarar badi, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugabancin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China