Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya, za ta kaddamar da shugaban kasar mai ci Goodluck Jonathan, a matsayin 'dan takararta a babban zaben kasar dake tafe a watan Fabarairun badi, yayin babban taron da ta fara a jiya Labara.
Tun dai cikin watan Oktobar da ya shude ne jagororin jam''iyyar ta PDP suka nuna amincewarsu ga takarar shugaban kasar mai ci. Yayin da a wannan karo ake fatan mika masa takardar takarar jam'iyyar a hukumce.
Babban taron na PDP dai na zuwa ne a yayin da ita ma babbar jam'iyyar adawa ta APC ke nata taron a birnin Legas, domin fidda wanda zai zamo mata 'dan takara a zaben na badi.
Tuni dai APCn ta tantance 'yan takara 5, da za su kara a zaben fidda gwani, wadanda suka hada da tsohon shugaban kasar janar Muhammadu Buhari, da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, sai kuma gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso, da na Imo Rochas Okorocha, da kuma shugaban jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah.
Ana dai sa ran bayyana wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ta APC a yau Alhamis. (Saminu)