Shugaban 'yan majalisun Najeriya, Aminu Tambuwal, ya sanar da fita daga jam'iyyar PDP a ranar Talata domin koma wa babbar jam'iyyar adawa ta APC, kafin zuwan zabubukan shekarar 2015. Mista Tambuwal ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a yayin zaman muhawarar 'yan majalisun a Abuja, babban birnin Najeriya, tare da bayyana cewa, ya bar PDP bisa wasu dalilai na siyasa. Domin zai tsaya takarar neman kujerar gwamnan jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya.
Ficewar mista Tambuwal ta kasance wani shan kaye na baya bayan nan ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda zai tsaya takarar zaben shugaban kasa na ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2015.
Jam'iyyar adawa ta APC na zargin shugaba Jonathan da kasawa wajen yaki da cin hanci da rashawa, da kasa magance matsalar kungiyar Boko Haram a arewacin kasar, da kuma kasa cika alkawuran kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki. (Maman Ada)