in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nigeria zai shiga zaben shugaban kasa a shekarar 2015
2014-10-24 13:19:48 cri

Shugaban kasar Nigeria mai rike da akalar mulkin kasar, Goodluck Jonathan, ya yanke shawarar ta tsunduma cikin fafutukar kara ganin an zabe shi a zaben shugaban kasar da za'a yi a shekarar 2015.

Kamar dai yadda wasu rahotannin kafofin yada labarai na kasar suka bayyana, shugaban kasar ta Nigeria ya yi shelar muradin shi na kara tsayawa neman kujerar shugabancin kasar a yayin wani taron shugabannin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, wanda aka yi a fadar shugaban kasar a Abuja jiya Alhamis.

A ranar Laraba ne jam'iyyar dake mulkin kasar ta Nigeria ta baiwa shugaban kasar Jonathan da sauran masu sha'awar shiga takarar shugabancin kasar damar sayen takardun dake nuna cewar, suna da muradin shiga cikin takarar shugabancin kasar a shekarar 2015, kuma an ba su damar yin haka har nan da ranar 30 ga watan Oktoba. Rahoton ya ce, Jonathan ya yi alkawarin a gaban shugabanin jam'iyyarsa cewar, zai sayi takardun shiga takarar zaben kamin cikar wa'adin da aka kebe.

Wata majiya daga fadar gwamnatin kasar ta ce, shugaban kasar Nigeria ya kafa wani kwamitin shugaban kasa na shelar tsayawarsa takarar a zaben shekarar 2015, kwamitin wanda ke karkashin shugabancin tsohon ministan tsaro na Nigeria Haliru Bello, an ba shi damar da ya zayyana shirye-shirye na share fagen fitowar shugaban kasar, karara ya bayyana muradinsa na neman a sake zaben sa. Ana sa rai shugaban kasar zai bayyana muradinsa tsakanin ranar 7 zuwa 15 ga watan Nuwumba mai zuwa.

A watan da ya gabata ne shugabannin jam'iyyar PDP suka tsai da shi a matsayin 'dan takarar zaben shugaban kasar jam'iyyar a shekarar ta 2015 saboda ayyukansa da suka ce na kawo ci gaba a cikin kasar ta Nigeria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China