Rahoton ya ce, a cikin rahoton da gwamnatin Amurka ta bayar, gwamnatin kasar Amurka ta maida kanta kamar kasar da ta fi yin fice a fannin kiyaye hakkin bil'adam, inda ta soki yanayin hakkin bil'adam da kasashen duniya da shiyya-shiyya kimanin 200 suke ciki.
Amma a sa'i daya, Amurka ta boye yanayin hakkin bil'adam da ita kanta ke ciki ta hanyoyi daban daban. A hakika dai, matsalar hakkin bil'adam da Amurka take fama da ita a bara ta yi tsanani sosai a fannoni da dama.
Wannan rahoto na 2013 ya bayyana matsalolin da Afirka ke fuskanta ta fannin take hakkin bil'adam daga fannoni daban daban, wadanda suka hada da karuwar yawan laifuffukan nuna karfi, da karuwar amfani da bindigogi ana harbe-harbe ba dalili, abin da rahoton ya nuna cewa yanayin tsaro ya tabarbare a kasar.
Sa'an nan, Amurka ta gudanar da shirin Prism, domin leken asiri na kasa da kasa, hakan ya keta dokokin kasa da kasa, tare da keta hakkin bil'adam.
Rahoton ya nuna cewa, a Amurka, akwai fursunoni da dama da akewa tsaron kadaici, wadanda yawansu ya kai mutum fiye da dubu 80. Irin wadannan masu laifi da ba barin su su yi mu'amala da kowa kan shafe tsawon lokaci, wasunsu ma kan kai har shekaru 40 cikin wannan hali.
Har wa yau, ana fama da matsalar rashin aikin yi a kasar Amurka, mutane da dama,basu da abin yi.
Rahoton ya kara da cewa ana ci gaba da nuna bambancin launin fata a Amurka, da bambanci jinsi kuma ba a ba da isasshen kulawa ga ikon yara ba. An samu ma'aikata yara da yawa a aikin noma a Amurka, hakan ya yi babbar illa ga lafiyarsu.
Baya ga haka, Amurka ta kasance kasar da ta fi take wa sauran kasashen duniya hakkin bil'adam, ganin yadda ta kai harin jirgin sama maras matuki sau da dama a Pakistan, Yemen da sauran kasashe, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jama'a masu dimbin yawa.
Amurka ba ta zartas ko shiga yarjejeniyar kiyaye ikon tattalin arziki, zamantakewar al'umma, da kuma al'adu ta duniya ba, haka kuma bata shiga yarjejeniyar kawar da nuna bambanci ga mata, da yarjejeniyar kiyaye ikon yara, da yarjejeniyar kiyaye ikon nakasassu da sauransu na MDD ba.
Baki daya wajen rubuta wannan rahoton yanayin hakkin bil'adam na Amurka na shekarar 2013, an kasa shi zuwa gida gida cikin har da kulawa da rayuwa da tsaron jama'a, kulawa da ikon jama'a da na siyasa, kulawa da ikon tattalin arziki da na zamantakewar al'umma da dai sauransu. (Fatima)