Wannan kalami na kasar na kunshe cikin wata sanarwar da hukumar tsaron kasar ta bayar a yau Lahadi tana mai cewa, yarjejeniyar kare hakkin bil-adama da kungiyar tarayyar Turai da Japan suka tsara wani abin kunya ne.
A ranar Talata ne kwamiti na uku na babban zaman taron MDD ya yanke kudurin da ya amincewa kwamitin sulhu da ya gabatar da kasar koriya ta arewa a gaban kotun hukunta mai laifuffuka ta duniya ICC saboda zargin keta hakkin bil-adama,kudurin da kasar ta yi watsi da shi.
Bugu da kari hukumar tsaron kasar koriya ta arewa ta yi gargadin cewa, sojojin kasar za su dauki tsauraran matakai don wargaza kamfel din da Amurka ke yi game da batun kare hakkin bil-adaman na kasar, inda ta ke nuna yatsa ga kasashen Amurka,Japan da kuma koriya ta kudu.
Ta ce, idan tura ta kai bango hakika kasashen uku za su dandana kudarsu, kuma MDD ba za ta iya daukar alhakin sakamakon abin da zai biyo baya ba.(Ibrahim)