in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamishinan kula da kare hakkin bil-adam na MDD zai ziyarci CAR
2014-03-18 09:55:16 cri

A yau Talata ne ake sa ran Navi Pillay, babban kwamishinan kula da kare hakkin bil-adam na MDD zai fara wata ziyara a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR.

Kakakin MDD wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce, yayin ziyarar jami'in, ana sa ran zai gana da shugabar rikon kwaryar kasar Catherine Samba-Panza, wakilan kungiyar AU, ECOWAS, kungiyar EU, shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU MISCA da kwamandojin MISCA da kuma dakarun kasar Faransa da ke kasar.

Ofishin kula da harkokin siyasa na MDD, ya ce, kasar Amurka ta shafe sama da shekaru 10 tana taimaka wa kasar, kuma yanzu haka tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD (BINUCA) na kasar a kokarin da ke na wanzar da zaman lafiya.

A watan Disamban shekara da ta gabata ce kasar ta tsunduma cikin rikice-rikice lokacin da mayakan Seleka suka kaddamar da hare-hare, lamarin da ya tilasta wa shugaba Francois Bozize barin kasar a watan Maris bayan da suka kwace Bangui, babban birnin kasar. Daga bisani aka kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin firaminista Nicolas Tiangaye, wanda aka damka masa alhakin maido da doka da oda tare da shirya zabe.

Ko da yake an ci gaba da yin tashin hankali a arewa maso gabashin kasar tun a watan Agusta, lamarin da ya cusa al'ummar kasar kusan miliyan 4.6 cikin mawuyacin hali, inda a ranar 10 ga watan Janairu, shugaban rikon kwaryar kasar na wancan lokaci Michel Djotodia da firaminista Tiangaye suka yi murabus.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China