in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun Cadfund ya samar da kudin kyauta na musamman ga kasashen yammacin Afirka uku dake fama da cutar Ebola
2014-11-05 16:26:49 cri

A jiya Talata 4 ga watan nan ne asusun Cadfund, dake karkashin shugabancin bankin raya kasa na Sin, ya shirya bikin ba da tallafin kudin kyauta domin yaki da cutar Ebola. Yayin taron an sanar da cewa, a madadin bankin, asusun zai samar da kudin musamman da yawansu ya kai dalar Amurka dubu 450 ga kasashe uku, wato Liberia, da Guinee, da Saliyo, domin taimakawa aikin da ake yi na yaki da cutar Ebola.

Sakamakon ci gaba da yaduwar cutar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka, wanda ke yin babbar barazana ga rayuwar jama'ar yankunan, da bunkasuwar tattalin arzikin al'ummarsu, da ma yanayin kiwon lafiya na duniya baki daya, kuma kasashen Guinee, da Liberia, da Saliyo ke kan gaba wajen fama da wannan annoba, ana iya cewa yunkurin hana yaduwar wannan cutar ta Ebola, da kuma shawo kanta sun zama kalubale bai daya ga kasashen duniya a fannin kiwon lafiya.

Yayin wannan taro shugaban bankin raya kasa na Sin, Mista Hu Huaibang ya yi jawabi yayin bikin, ya ce,

"yanayin yaduwar cutar Ebola da ake ciki a wasu kasashen Afrika na jawo hankalin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, ciki har da ma'aikatan bankinmu. Domin nuna goyon baya ga gwamnatocin kasashen wajen yaki da cutar Ebola, bankinmu ya umurci asusun Cadfund da ya samar da kudin kyauta har dalar Amurka dubu 150 ga ko wace kasa, cikin kasashen uku, wato Guinee, da Liberia, da Saliyo. Muna fatan samar da taimakonmu ga jama'ar Afirka wajen hana ci gaban yaduwar wannan cuta, muna kuma fatan ta wannan hanya za mu iya zaburar da hukumomi, da masana'antu masu yawa wajen nuna goyon baya ga jama'ar Afirka, ta yadda za a iya kara masu kwarin gwiwa wajen yaki da cutar."

Jakadan kasar Liberia dake kasar Sin, mista Dudley Mckinley Thomas, a madadin jakadun kasashen uku ya yi jawabi a yayin bikin, inda ya yi godiya matuka ga tallafin da bangaren Sin ya bayar, ya kuma nuna yabo kwarai kan sahihiyar zumunta ta jama'ar kasar Sin ga jama'ar Afirka.

Ya ce,

"Muna muku godiya kan babban tallafin da kuka ba mu. Wannan matakin da bankin raya kasa na Sin, da asusun Cadfund suka bayar ya nuna cewa, jama'ar kasashen yammacin Afirka ba su kadai ne ke fama da wannan cuta ta Ebola ba, ya kuma bayyana cewa, jama'ar kasar Sin sun nuna kulawar jin kai, da sahihin zumunci ga kasar Liberia da sauran 'yan uwa kasashen Afrika wadanda ke fama da cutar Ebola, wanda hakan zai taimakawa jama'ar kasashen Afirka wajen cimma nasarar yaki da cutar."

A nasa bangaren, mataimakin sashen kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Wang Shiting a jawabinsa cewa ya yi ba da tabbaci kan nauyin da al'umma, da masana'antun kasar Sin ke fatan saukewa, ciki har da gudummawar bankin raya kasa game da kasashen na Afirka muhimmin batu ne. Ya ce,

"wannan matakin da bankin raya kasa na Sin ya dauka ya bayyana cewa, akwai zumunci sahihi a tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasashen yammacin Afirka. Na yi imanin cewa, wadannan tallafin kudi za su taka rawa kan yaki da cutar Ebola a kasashen uku. Muna kuma fatan masana'antun kasar Sin mafi yawa za su bayar da taimakonsu ga gwamnatoci da jama'ar kasashen Afirka dake fama da cutar, domin taimaka musu wajen cimma nasarar yaki da cutar cikin hanzari, da kuma sake gina gidajensu."

Mista Wang ya ci gaba da cewa, tun bayan barkewar cutar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka, gwamnatin kasar ta Sin ta riga ta samar da taimakon gaggawa har karo hudu, wanda darajarsa ta kai kudin Sin RMB miliyan 750 ga kasashen da abin ya shafa, domin yaki da cutar, da kuma kasashe guda goma masu makwabtaka da su, har ma da kungiyoyin duniya da na shiyyar, ciki har da MDD, da kungiyar lafiya ta duniya (WHO), da kuma kawancen kasashen Afirka (AU) da dai sauransu. Haka zalika gwamnatin kasar Sin ta aike da kwararru da likitoci sama da 700 zuwa yankunan, a gaskiya hakan ya nuna manufar hadin kai da Sin ke bi game da kasashen Afirka, wato dai batun nuna gaskiya ga abokanta na kasashen Afirka, da gudanar da hakikanin hadin kai, da nuna shakuwa da juna wajen zumunci, da ma nuna kwazo wajen warware sabbin matsalolin dake bullowa a yayin hadin gwiwar cinikayya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China