Da karfe 4 da rabi a ranar 3 ga wata, wata girgizar kasa mai karfin maki 6.5 bisa ma'aunin Richter, ta auka a gundumar Ludian dake lardin Yunnan, inda ta haddasa mutuwar mutane da dama.
Ya zuwa karfe 7 na ranar 4 ga wata, mutane 373 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasar. A halin yanzu, ana ci gaba da yin kididdiga kan yanayin yankin dake fama da girgizar kasar.
Bisa umurnin da shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang suka bayar, hukumomin majalisar gudanarwar kasar da hukumomin yankin da bala'in ya faru sun dauki matakan gudanar da ayyukan bada ceton gaggawa. (Zainab)