in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta fara jigilar 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu dubu 15 a Habasha
2014-11-19 15:44:26 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta fara jigilar kimanin 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu da yawansu ya kai dubu 15, domin canza musu wurin zama saboda an sami ambaliyar ruwa, inda suke zaune a yammacin kasar Habasha, in ji Xinhua jiya Talata.

Wata sanarwa daga hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce, rukuni na farko na 'yan gudun hijira 125 sun tashi daga tashar Matar way a ranar Litinin inda suka durfafi kogin Baro, a inda daga nan suka yada zango a cibiyar Itang, inda a nan ne suka kwana, kuma gari wayewa suka tunkari sansanin 'yan gudun hijira na Pugnido.

Ana sa rai 'yan gudun hijirar za su hallara a wannan sansanin, inda dama akwai wasu 'yan gudun hijirar kimanin dubu 45 dake zaune a sansanin wanda kuma galibinsu 'yan Sudan ta Kudu.

A ranar Talata, za'a kara aikewa da 'yan gudun hijira 29 masu bukatar kulawa wadanda suka hada da mata masu ciki da masu shayarwa, da kuma masu makanta da tsaffi.

Kawo ya zuwa yanzu 'yan gudun hijira dubu 190 daga Sudan ta Kudu, suka nemi mafaka a yankin Gambella dake Habasha, tun bayan da rikici ya balle a kasarsu a tsakiyar watan Disamban shekara ta 2013, in ji UNHCR.

Hakazalika wasu karin 'yan gudun hijira kimanin 100 suna tsallake kan iyaka suna shiga kasar Habasha daga Sudan ta Kudu ko wace rana.

Sai dai kuma sabbin 'yan gudun hijirar suna kokawa a game da matsalar karancin abinci da rashin matakan tsaro da kuma ballewar rikici a wadansu lokuta tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China