Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta ce, tana jigilar karin kayayyakin abinci ta jirgin sama daga Dubai kai tsaye zuwa Sudan ta Kudu domin ba da agaji ga mutane kimanin dubu 100 wadanda suka rasa muhallansu a cikin wani hali da ake kusa da fara ruwan sama a kasar.
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce, ta kara kaimi ne wajen ganin ta rarrabawa 'yan gudun hijirar barguna, tabarmin barci, bokatai da kuma sauran kayayyakin agaji wadanda za'a rarraba a jihohin Unity, Upper Nile da Jonglei.
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD ta kara da cewar, alkaluman kididdiga sun nuna cewar, kimanin mutane dubu 923 ne suka rasa muhallansu a cikin kasarsu ta gado. Kamar dai yadda hukumar ta ce su wadannan mutanen sun rarrabu ne a wasu sansanoni 174 da aka shirya a inda shi sansanin 'yan gudun hijirar dake Upper Nile ya fi samun cikowa.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, fiye da mutane dari 293 ne suka zamanto 'yan gudun hijira a kasashe makwabta, tun daga watan Disambar shekarar bara lokacin da rikici ya barke tsakanin kungiyoyi masu goyon bayan gwamnati da kuma kungiyoyi na 'yan adawa a Juba. (Suwaiba)