in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta yi kiran da a samar da kayayyakin agaji a CAR
2014-10-15 14:53:04 cri

Ofishin babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na MDD (UNHCR) ya yi gargadin cewa, fadan baya-bayan da ya barke a Bangui, babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) ya kawo cikas ga ayyukan jin kai da ake gudanarwa a kasar.

Hukumar ta UNHCR ta bayyana cewa, fadan wadda ya shafi fararen hula, ma'aikatan agaji da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD ya kasance hare-hare mafi tayar da hankali da aka taba kaiwa ma'aikatan jin kai da ke kokarin kaiwa ga mutanen da suka rasa muhallansu a Bangui da kewaye.

Don haka kakakin hukumar ta UNHCR Melissa Fleming ta yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da juna da su mutunta ayyukan jin kai tare da barin hukumomin agajin da ke aikin taimakawa dubban mutanen da rikicin ya dai-daita da ke matukar bukatar agaji isa gare su.

Alkamun na nuna cewa, akwai kimanin mutane 410,000 da rikicin kasar Afirka ta Tsakiya ya wargaza, ciki har da sama da mutane 60,000 a Bangui da kuma wasu kimanin 420,000 da suka tsallaka zuwa kasashe makwabta don neman mafaka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China