in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR za ta kara yawan kayan tallafi ga 'yan gudun hijirar Iraqi
2014-08-20 10:19:57 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta ce, ta shirya tura karin kayayyakin agajin jin kai zuwa kasar Iraqi, domin sassauta halin matsi da mutane kimanin rabin miliyan, wadanda suka kauracewa gidajensu ke ciki.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDD Stephen Dujarric ya ce, za a yi jigilar wadannan kayyayaki ne tsahon kwanaki 10 masu zuwa, inda ake fatan shigar da su Iraqin ta kasa da sama, daga kasashen Jordan, da Turkiyya, da kuma hadaddiyar daular Larabawa. Dujarric ya ce, kayan da ake fatan aikewa da su sun hada da tantuna, da kayan abinci da kuma na amfanin yau da kullum.

Game da kudaden da za a yi amfani da su wajen samar da wadannan kayayyaki kuwa, kakakin MDDr ya ce, kasar Saudia ta yi namijin kokari, inda ta samar da kudi har dalar Amurka miliyan 500 ga hukumar, baya ga karin tallafi daga kasashen Amurka da Birtaniya da Japan da wasu kasashen Turai masu tallafawa ayyukan hukumar.

A cikin kasar ta Iraqi kuwa, yanzu haka hukumar abinci ta duniya WFP, ta ce, ta kara yawan tallafin da take baiwa dubban jama'a, tun daga tsakiyar watan Yunin da ya shude, wadanda suka hada da kiristoci, da musulmi da fadace-fadace suka kora, da ma Yazidawa da hare-haren 'yan kungiyar ISIS ya tilasawa barin gidajensu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China