in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rikon kwarya a Zambiya ya yi kiran 'yan kasar ga zaman lafiya
2014-10-30 10:47:28 cri

Mukadashin shugaban kasar Zambiya, Guy Scott, dake rike da mukamin shugaban kasa bayan mutuwar shugaba Michael Sata, ya kira a ranar Laraba ga zaman lafiya da hadin kan kasa. Mista Scott, da zai jagoranci kasar a tsawon watanni uku masu zuwa har zuwa lokacin da aka zabi wani sabon shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, ya sanar da zaman makoki na kasa da aka fara a ranar Laraba, tare da nuna cewa, zai gabatar da wani cikakken jadawali a nan gaba domin karin haske. A cikin jawabinsa zuwa ga 'yan kasa a gidan talabijin na kasa, shugaban rikon kwarya ya yi kiran al'ummar kasa da su girmama lokacin zaman makoki cikin zaman lafiya da natsuwa, tare da bin doka da oda.

Haka kuma ya bayyana cewa, zai sanya ido cikin adalci kan tsarin zaben sabon shugaban kasa bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa. Gwamnatin Zambiya ta yi zaman taro jim kadan bayan rasuwar mista Sata tare da na da mista Scott a matsayin shugaban rikon kwarya, a cewar ministan shari'a Edgar Lungu, dake rike da mukamin shugaban kasa tun lokacin da mista Sata ya yi tafiya zuwa London domin binciken lafiya a ranar 20 ga watan Oktoba. Wani babin kundin tsarin mulkin kasar dake magana kan asilin ma'aifa, ya tilastawa 'dan takarar zaben shugaban kasa ya zama ma'aifansa biyu an aife su a Zambiya, wanda hakan ya haramtawa mista Scott shiga takarar zaben shugaban kasa. Mista Scott mai shekaru 70 da aifuwa, 'dan asilin kasar Scotland ne kana ma'aifansa ba'a aife su ba a Zambiya. Kuma shi ne farar fata na farko da zai jagoranci wannan kasa tun bayan samun 'yancinta daga hannun kasar Burtaniya a shekarar 1964. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China