Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ce, mutuwar shugaban kasar Zambia Michael Sata ta sosa ranshi matuka.
A yayin wani taron manema labarai a mako mako, kakakin magatakardan MDD Stephane Dujarric ya ce, Ban ki-moon ya kuma mika gaisuwar jaje ga gwamnati da jama'ar kasar ta Zambia da kuma iyalan shugaban kasar.
Tun farko gwamnatin Zambia ta bayyana cewar, Sata ya rasu bayan gwajin lafiyarsa a wani asibitin London dake Britania, sakamakon wata cuta da ba a bayyana nau'inta ba.
Tun a watan Yuni dai ne, aka shiga damuwa a game da lafiyar Michael Sata, tun bayan da ya fito a cikin talabijin din kasar da siffar maras lafiya.
Marigayi Michael Sata shi ne shugaban kasar Zambia na biyu da ya rasu a kan gadon mulki, a can baya tsohon shugaban kasar marigayi Levy Mwanawasa ya rasu a shekarar 2008, a yayin da yake halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afrika a Masar. (Suwaiba)