A ranar Laraba ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cikin wata sanarwar aka raba wa manema labarai cewa, wasu ministocin kasar guda 7 sun bayyana aniyarsu ta sauka daga mukamansu don neman tsayawa takara a mukaman siyasu a jihohinsu.
Ministoci sun bayyana aniyar sauka daga mukaman nasu ne a yayin taron majalisar zartarwar kasar na mako-mako da aka gudanar ranar Laraba da safe.
Ministocin da suka sauka daga mukaman nasu sun hada da ministan watsa labaran kasar Labaran Maku, karamin minista a ma'aikatar cinikayya da zuba jari Samuel Ortom, karamin minista a ma'aikatar tsaro Musiliu Obanikoro, da kuma ministan lafiya Onyebuchi Chukwu.
Sauran sun hada da karamin minista a ma'akatar ilimi Nyesom Wike, ministan kwadago da ingancin aiki Emeka Wogu, da karamin minista a ma'aikatar kula da yankin Niger Delta Dairus Ishaku.
Wata majiya a fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa, dole ne dukkan ministocin su sauka daga makamansu idan har suna son neman tsayawa takarar makuman gwamnoni a jihohin nasu.
A watan da ya gabata ne shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya baiwa dukkan ministocinsa dake son tsayawa takara a zaben kasar da ke tafe wa'adin zuwa ranar 20 ga watan Oktoba da su ajiya mukamansu domin su cimma burinsu.
A ranar 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2015 ne za a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya. (Ibrahim)