Gwamnan jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa, zai shiga zaben shugaban kasa na shekarar 2015, in ji daya daga cikin manyan na hannun daman gwamnan a ranar Litinin.
Mista Kwankwaso, wanda a da yake mamba na jam'iyyar PDP mai mulki, ya bayyana niyyarsa a ranar Alhamis na shiga zaben shugaban kasa a matsayin 'dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya, wato sabuwar jam'iyyarsa, in ji Olisaemeka Akumaki, darektan cibiyar yakin neman zabe na gwamnan a gaban manema labarai a birnin Abuja. (Maman Ada)