Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana matan karkara a matsayin kashin bayan samun ci gaba mai dorewa yayin da duniya ke yunkurin cimma manufofin bunkasuwa bayan shekara ta 2015, da kuma yarjejeniyar bai daya game da canjin yanayi.
Mr. Ban ya bayyana hakan ne yayin murnar ranar matan karkara ta duniya da aka yi jiya Laraba 15 ga wata.
Ya ce, duk da cewa matakan da ke karkara na zaune cikin kangin talauci, bala'u daga indallahi da sauran nau'o'i na barazana, duk da haka matan karkara suna da babban nauyi a kokarin da ake na cimma nasarori a kamfel-kamfel din da ake a duniya.
Mr. Ban ya ce, matan karkara suna da matukar muhimmanci wajen sa kaimi ga ayyukan da ake gudanarwa game da cimma manufofin muradun karni, dacewa da sabbin manufofi don samun ci gaban mai dorewa da kuma cimma yarjejeniyar bai daya game da canjin yanayi.
Alkaluman MDD na nuna cewa, galibin matan da ke zaune a yankunan karkara na dogaro ne kan albarkatun kasa don rayuwa, yayin da suka kunshi 40 cikin 100 na wadanda ke aikin kwadago a bangaren aikin gona a kasashen da suka ci gaba.
Don haka ya ce, kamata ya yi a samar wa matan karkara kayayyakin aikin gona da sarrafa albarkatun kasa na zamani, ta yadda daga baya za su bayar da karin gudummawa wajen kawar da yunwa, tare da inganta rayuwar al'ummominsu, ta yadda za su iya dacewa da tasirin canjin yanayi, wadda daga karshe kowa zai amfana. (Ibrahim)