in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a sabunta kudurin inganta lafiyar mata da yara
2014-09-26 10:10:28 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan 25 ga wata ya bukaci a sabunta kuduri da wani mataki da zai inganta cigaban da ake da shi yanzu haka a bangaren lafiyar yara kanana da mata a fadin duniya baki daya.

Mr. Ban a lokacin da yake jawabi wajen taro mai taken "ko wane aiki na mata da yara" da aka yi yayin babbar muhawarar ta taron majalissar da a kan yi na shekara shekara, ya ce, a karon farko cikin tarihi, an samu damar da za'a iya hana mutuwar da ka iya faruwa saboda rashin kula ga yara kanana da mata a cikin al'umma.

Wannan taron mai taken "ko wane aiki na yara da mata" dai, an kaddamar da shi ne a watan Satumba na shekara ta 2010, kuma yana da nufin ceto rayuwan mata da yara kananan kusan miliyan 16 nan da shekara ta 2015.

Babban magatakardar ya lura cewa, wannan kokari a wannan shirin ya samu nasarar rage mutuwar yara kananan wadanda ba su cika shekaru 5 ba a duniya cikin sauri fiye da sauran lokuta a cikin shekaru 20 a ko wace rana, in ji shi, kusan yara dubu 17 kan tsira daga mutuwar da za'a iya karewa, sannan mutuwar iyaye mata ma ta ragu da kusan rabi tun daga shekara ta 1990.

Mr. Ban har ila yau ya ce, ya kamata al'ummomin duniya su ba da kariya ga wadannan jinsu da ba su da karfin jiki sosai su kuma nuna juriya bisa ga kalubalolin da suke fuskanta da suka hada da sauyin yanayi, tsabtataccen ruwan sha, ba da ilimi, muhalli mai tsabta, abinci mai gina jiki, 'yancin 'dan adam da ya shafi lafiyar mata da yara kanana. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China