Majalisar dinkin duniya ta bukaci a ranar Talata, kasashen Afrika da su gudanar da gyare-gyare a bangaren haya, ta yadda za'a canja bunkasuwar unguwannin talakawa a yankunan birane.
Claudio Acioly, darektan reshen cigaban karfin MDD da muhallin jama'a, ya bayyana a yayin taron shiyya kan haya a Nairobi cewa, bunkasuwar unguwannin talakawa na tafiya daidaita da cigaban birane cikin sauri. Akwai manufofin siyasa dake ingiza wasu tsare-tsaren ba da haya da cinkoson jama'a cikin gidaje, in ji mista Acioly a yayin bikin rufe taro kan haya a Afrika, da aka kwashe kwanaki biyu ana yinsa wanda kuma ya hada masu ruwa da tsaki a bangaren haya a Afrika, domin tattauna cigaban kasuwannin haya bisa doka.
Mista Acioly ya bayyana cewa, manufofin siyasa a wannan fanni ya kamata a fadada manyan bukatu, ba da haya, farashi da ka'idodi da matakai a wannan fanni da sauransu. Haka kuma da kirkiro manufofin haya, tare da manufofin tsara birane, ta yadda za'a iyar cike karancin gidajen haya. (Maman Ada)