in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa wata gamayyar kamfanonin dillancin labaran Afrika
2014-10-15 14:07:37 cri

Mahalarta dandalin farko na kamfanonin dillancin labaran Afrika, da kamfanin dillancin labarai na kasar Morocco (MAP) ya shirya, sun kafa a ranar Talata a birnin Casablanca da wata gamayyar Atlantik ta kamfanonin dillancin labaran Afrika (FAAPA). FAAPA na da burin yaukaka wata muhimmiyar dangantaka da bunkasa huldar aiki tsakanin kamfanonin dillancin labaran na yankunan Afrika, bunkasa musanyar labarai da ayyukan kafofin watsa labarai tsakanin mambobinta, da karfafa 'yancin shawagin labarai a shiyyar, tattara, gyarawa da watsa labaran da suka shafi wadannan kasashe yadda ya kamata.

Da kuma kasancewa wata hanyar shirya tarurukan karawa juna sani da na ba da ilimi kan batutuwan dake janyo hankali da muhimmanci ga junansu, aza tubalin wata huldar dangantaka mai alfanu da taimakon juna daga dukkan fannoni, ba da kariya, tare da bunkasa moriyar mambobin FAAPA da kuma karfafa musanya da kwarewa, baya ga tattaunawa da kuma samun ra'ayi guda a cikin dandalin shiyyoyi da na kasa da kasa.

Sauran kamfanonin dillancin labarai da suka kafa FAAPA sun hada kamfanin dillancin labaran kasar Senegal (APS), kamfanin dillancin labaran kasar Guinea (AGP), kamfanin dillancin labaran kasar Kamaru (Camerpresse), kamfanin dillancin labaran kasar Togo (ATOP), kamfanin dillancin labaran kasar Guinea-Bissau (ANG), kamfanin dillancin labaran kasar Ghana (GNA), kamfanin dillancin labaran kasar Mali (AMAP), kamfanin dillancin kasar Burkina-Faso, kamfanin dillancin labaran kasar Nijar (ANP), kamfanin dillancin labaran kasar Afrika ta Tsakiya (ACAP) da kamfanin dillancin labaran kasar Chadi (ATPE). (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China