in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Afrika na mai da hankali a Marrakech kan dangantakar Kudu da Kudu
2014-10-16 14:08:01 cri

Dandalin cigaban Afrika (ADF-IX) da ya gudana a karon farko a waje da Addis-Abeba, babban birnin kasar Habasha, daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Oktoba a Marrakech a karkashin jagorancin kwamitin tattalin arzikin kasashen Afrika (CEA), ya mai da hankali kan matsalar dangantakar Kudu da Kudu, da mahalarta dandalin suka dauka a matsayin wani ginshikin cigaban nahiyar Afrika. Kwararru a fannin tattalin arziki sun bayyana a yayin taron muhawara kan sabbin dabarun dangantaka a maimaikon dabarun dangantaka na gargajiya tsakanin Arewa da Kudu, wadanda suka rika dogaro kan dokar mai karfi, kuma babu wani alfanu ga bangarorin biyu. A kwana na biyu na wannan taron kasa da kasa, mahalarta sun kira wajen kafa wani tsarin doka da ya dace domin bunkasa zuba jari a Afrika.

A yayin wannan haduwa, Ali Abou Sabaa, wani jami'in bankin raya Afrika (BAD), ya tabbatar da cewa, an yi kiran kasashen Afrika da su yi dogaro da albarkatun kasashensu domin daidai bunkasuwa mai karfi da wadata.

Ya kamata, kasashen Afrika su cimma wasu manufofi masu nagarta da za su taimaka wa fadada gidauniyar haraji, in ji mista Sabaa tare da bayyana cewa, kudaden haraji da ake samu sun kasancewa daya daga cikin muhimmiman hanyoyin samun kudade a cikin gida, kuma wannan fannin yana cigaba da kyautatuwa a Afrika.

A nasa bangare, babban darektan bankin kasar Morocco na kasuwancin waje (BMCE Bank), Brahim Benjelloun Touimi, ya nuna cewa, Afrika na fuskantar wani kalubale na kokarin kaucewa yin dogaro da taimakon kungiyoyin cigaba da daukar mataki game da iyakokin siyasa da aka gada daga kasashe 'yan mulkin mallaka domin farfado da cigaban nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China