Wata majiyar sojan kasar Kamaru ta tabbatar da cewa, dakarunta sun halaka mayakan Boko Haram 27 a wata arangama da suka yi a kauyukan Amchide da Limani da ke lardin arewa mai nisa.
Majiyar da ta bukaci a sakaye sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe sojojin Kamaru 8 a yayin arangamar yayin da aka lalata motocin Boko Haram guda biyar. Ko da yake ma'aikatar tsaron kasar kamaru ta ce, 'yan Boko Haram 39 aka kashe yayin wannan ba ta kashi, sannan ba ta bayyana asarar da bangaren sojojin na Kamaru suka yi ba.
Wasu bayanai kuma na cewa, mayakan na Boko Haram sun halaka sojojin Kamaru 8, kana wasu 11 sun jikkata.
Kasar Kamaru dai ta hada kan iyaka da Najeriya na kusan sama da kilomita 2,000 wurin da mayakan na Boko Haram suka kaddamar da hare-hare tun a shekara ta 2009. (Ibrahim)