A ranar Lahadin nan 27 ga wata, 'yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da uwar gidan mataimakin firaministan kasar Kamaru Amadou Ali a wani hari da suka kai a garin Kolofata dake arewacin kasar.
Kamar yadda ministan yada labaran kasar, kuma kakakin gwamnati Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar da cewa, an kai harin ne a gidan jami'in gwamnatin dake kusa da kan iyaka da Nigeriya, sakamakon haka, suka yi awon gaba da uwar gidan shi.
Haka kuma an yi awon gaba da wani babban malamin addini a kasar Seini Boukar wanda aka fi sani da Lamido, in ji ministan lokacin da yake tabbatar da wannan lamari ga Xinhua ta wayar tarho.
A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a lokacin wannan hari, kamar yadda rundunar sojin kasar suka tabbatar. (Fatimah)