Ministan sadarwar kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya ce, dakarun kasarsa sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar Boko Haram sama da 100, yayin wani dauki ba dadi da bangarorin biyu suka yi a ranar Asabar din karshen makon jiya.
Bakary ya ce, dakarun sassan biyu sun kwashe sa'o'i suna musayar wuta a garin Fotokol dake arewacin iyakar kasar ta Kamaru da Najeriya. Kana babu wani sojin kasar da ya rasu sakamakon dauki ba dadin.
Game da hakan ministan sadarwar ya jinjinawa kwazon da dakarun sojin Kamarun suka nuna wajen tirsasa mayakan Boko Haram din ja da baya zuwa yankin Najeriya.
Kasashen Kamaru da Najeriya dai sun hada kan iyakar da ta kai nisan kilomita 2,000. Tun kuma farkon shekarar 2013 da ta gabata, kasar ta Kamaru ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga 'ya 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda suka taba kame wani Bafaranshe a wani yanki dake arewacin kasar. (Saminu)